Show cover of Najeriya a Yau

Najeriya a Yau

Shiri ne na minti 15 dake duba na tsanaki, da nazari mai gamsarwa, tare da tsokaci mai amfanarwa, a kan batutuwan da ke ɗaukar hankali a lamuran yau da kullum.

Tracks

Dalilin Da Kotuna Ke Yanke Hukunci Mabambanta Kan Shari’a Iri Ɗaya
Ba shakka dokokin kasa iri guda ne a duk inda ake a Najeriya.Sai dai ana yawan samun kotuna da yin mabambantan matsaya kan shari’a iri guda a lokuta daban-daban. Ko me ya jawo haka?Shirin Najeriya a Yau ya duba abin da ya sa kotuna ke yanke hukunci daba-daban kan shari’a iri guda.
14:57 4/19/24
Me Ya Sa ‘Yan Kasuwa Suka Ƙi Karya Farashi Duk Da Karyewar Dala?
Ana ta murnar dalar Amurka na karyewa watakila a samu saukin kayan masarufi.Sai dai a ganin wasu yadda ‘yan kasuwa suke azamar tsawwala kudi idan ta tashi ba su yi hakan ba a yayin da take saukowa.Shirin Najeriya a Yau ya duba dalilin da ya zama wajibi ‘yan Kasuwa su sauke farashin kayayyaki.
15:15 4/18/24
Wa Ke Da Ikon Dakatar Da Ganduje A Jam’iyar APC?
An shiga saƙe-saƙe game da mutanen da suka yi ikirarin dakatar da Ganduje daga jam’iyar APC tun daga matakin mazaba.Sai dai uwar jam’iyar ta yi watsi da hakan, inda kuma daga bisani suka zargi jami’iyar adawa.To amma ko da ace za a dauki irin wannan matakin, wa ke da hurumin dakatar da shugaban jamiyar APC na kasa a dokance? Shirin Najeriya a Yau na da karin bayani.
14:58 4/16/24
Albashin Da Ya Kamata A Riƙa Biyan Ma’aikaci A Wannan Yanayi
Yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa ya sa komai ya sauya amma banda albashin ma’aikata.Akwai mahimman abubuwan da masu daukar albashi ba su iya yi saboda ma’aikatu da hukumomi sun kasa matsawa da albashinsu gaba.Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan abin da ya kamata mutum ya fara dubawa ta fannin albashi kafin karbar aiki.
12:03 4/15/24
Shin Ya Dace Mace Ta Fara Sitta-Shawwal Kafin Biyan Bashin Ramadan?
Wane lokaci ya fi dacewa mutum ya fara azumin sitta-shawwal?Ana yawan shiga rudani kan hakan, da kuma tunanin cewa mace wadda ake binta bashin azumin Ramadan ko ya kamata ta dauki azumin kafin biyan bashi?Shirin Najeriya a Yau na dauke da karin bayani da wasu batutuwan da ya kamata ku sani game da azumin na kwanaki shidan bayan karamar Sallah.
13:02 4/12/24
‘Da Ƙyar Muka Iya Cefanen Sallah Bayan An Sauko Idi’
Matsin rayuwa yana daga cikin abin da ya hana mutane da dama yin shagali da wannan karamar Sallah.Wasu ma basu iya yin cefanen Sallah na abincin da za a ci ballantana sabbin dinkuna.Shirin Najeriya a Yau ya zagay wasu jihohu domin yadda mutane suka yi Sallah cikin matsin rayuwa.
14:07 4/11/24
Wani Tela Ya Tsere Saboda Rashin Gama Ɗinkunan Sallah
Teloli iyayen haɗa gwarama! An saba kai ruwa rana a kowace Sallah idan teloli suka sha ta fi karfinsu.Sai dai ba saban ba, wani telan da muka zanta da shi ya ce ya kammala dinkunan da ya karba kakaf yayin da wani ya tsere ya bar masu kaya da wayyo!Shin wadanne dabaru ya kamata tela ya yi amfani da su wajen ganin ya sallami kowa? Shirin Najeriya a Yau na dauke da karin bayani.
13:43 4/9/24
Mutanen Da Aka Haramtawa Cin Zakkar Kono
Shin a wane lokaci aka yi umarnin fitar za Zakkar Fidda Kai?Malamai sun ce wannan Zakka tana da matukar mahimmanci ga masu hali kuma akwai lokacin da aka kayyade a fitar da ita; in ba haka ba kuma ta zama sadaka.Shirin Najeriya a Yau ya duba matakan fidda Zakatul-Fitr da mutanen da aka haramtawa cin ta.
13:13 4/8/24
Me Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Tsarin Raba Wutar Lantarki?
Tun bayan da aka kara kudin wutar lantarki mutane ke ta korafi game da yadda aka rarraba tsarin.Amma har yanzu wasu na cewa ba su fahimci yadda tsarin yake tafiya ba da kuma yadda lamarin ke neman shafar rayuwarsu matuƙa.Shirin Najeriya a Yau ya tattaun kan abubuwan da ya kamata ku sani game da sabon tsarin rabon lantarkin.
15:29 4/5/24
Yadda Za Ku Gane Daren Lailatul-Ƙadri Cikin Sauƙi
Akwai abubuwa na musamman da aka fi son a roƙa a irin wannan dare.Yawanci an fi maida hankali a ranakun wutiri daga 25 zuwa 29, duk da yake malamai na ba da shawarar a yi ibada sosai a dukkanin ranakun goman karshe.Shirin Najeriya a Yau ya tattauna da malamai gameda alamomin gane daren lailatul-ƙadri da abin da aka fi son bawa ya roƙa a ciki.
14:28 4/4/24
Matakan Kariya Daga Ɓata Gari A Lokacin Zuwa Tahajjud
Yanayin tsaro na jefa fargaba a zukatan wasu Musulmi da ke zuwa sallar dare ta Tahajjud.Wasu ɓata gari kan yi amfani da wannan damar da mutane ke fita tsakar dare domin aikata musu abin da bai dace ba.Shirin Najeriya a Yau ya duba wasu matakai na tsaro da za ku dauka domin kare kanku daga fadawa matsala.
13:41 4/2/24
Mutuwar Zuciya Ce Ta Jefa Matasa Harkar Kirifto
Shin a ganinku me ya sa matasa 'yan soshiyal midiya suka dukufa a harkar nan ta kirifto musamman 'mining' ?A yanzu haka da dama ne cikin matasan ke jiran ta fashe domin su kudance, sai dai akwai masu yi wa irin wadannan matasa kallon masu raunin zuciya.Shirin Najeriya a Yau ya tattauna da masu harkar mining da kuma masana kirifto kan abin da ya kamata ku sani kafin ku fara hakowa.
15:45 4/1/24
Illolin Yawaita Amfani Da Soshiyal Midiya A Ramadan
Yawan amfani da Soshiyal Midiya na haifar da gane-ganen abubuwan da ba su kamata ba.A lokacin Ramadaan yana da kyau mutum ya yi kokarin kaucewa duk wani abin da zai raunana mishi azumi.Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan abin da zai faru da ku idan kuka yawaita amfani a da soshiyal midiya a lokacin Ramadan.
12:51 3/29/24
Makomar Mutanen Da Aka Wanke Daga Zargin Alaƙa Da Boko Haram
Mutum sama da 300 aka saki ga gwamnatin jihar Borno a satin nan bayan wanke su daga zargin kungiyar Boko Haram.An dade ana tsare da su tsawon shekaru amma sai yanzu aka gano ba su da hannu. To amma me dokar kasa tace game da irin wannan tuhuma bayan an gano gaskiya?Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari kan halin da aka jefa su da kuma yadda doka za ta yi musu adalci.
14:18 3/28/24
"Shekara 8 Ina Tara Kuɗin Hajji Amma Yanzu Dole Na Fasa Zuwa"
Za a  iya cewa aikin Hajji a Najeriya sai ga mai rabo, domin tun bayan bullar labarin hukumar alhazan Najeriya NAHCON na cewa an yi ɗori kan kudin da aka ware a baya ake ta ƙorafi.Tuni wasu maniyyatan suka ce sun cire rai a yanzu, amma kuma hukumar ta ce akwai dalilan da babu yadda ta iya da su ne.Shirin Najeriya a Yau ya duba matakin, da wasu suka ce yana neman hana talakan Najeriya zuwa aikin Hajji.
13:53 3/26/24
Yadda Gwamnati Ta Kasa Miƙa Ɗaliban Kuriga Ga Iyayensu
An shafe tsawon wunin jiya Lahadi ana  zaman jira da dakon isowar daliban Kuriga da gwamnatin jihar Kaduna tace ta ceto.Saidai daga bisani, ba tare da wani cikakken bayani ba an umarci iyayen yaran su sake dawowa a yau Litinin domin amsar ‘ya’yan nasu.Shirin Najeriya a Yau ya duba abin da ya sa gwamnatin ta dauki wannan mataki ba tare da wani cikakken bayani ba.
14:47 3/25/24
‘Kimiyya Ake Buƙata A Fannin Shari’a Ba Ƙarin Albashin Alkalai Ba’
Fannin shari'a musamman alkalai a matakin tarayya sun samu kari kan albashinsu na baya.Ana ganin hakan zai samar da sauyi ga fannin shari'a da kuma dakile cin hanci ta wasu fannin, ko da yake wasu na ganin ba abin da ake bukata a fannin a yanzu ba kenan.Shirin Najeriya a Yau ya duba sauyin da karin albashin zai iya haifarwa a kasar.
15:53 3/22/24
Illar Shiga Jerin Sunayen Masu Ɗaukar Nauyin Ta'addanci
'Yan kasa sun jima suna kalubalantar gwamnatin tarayya ta ayyana sunayen masu daukar nauyin ta’addanci.Watakila gwamnatin ta duba wannan batu domin kamar yadda wasu suka ji a labari, ta bayyana sunan Tukur Mamu na jihar Kaduna da wasu mutane 14 waɗanda ɓaro-ɓaro ba za a iya cewa ta ambaci suna ba.Shirin Najeriya a Yau ya duba matakan doka kan ayyana sunan wanda aka samu da daukar nauyin ta’addanci.
14:22 3/21/24
Me Ya Sa Mutane Suka Daina Shafa Turarukan Kamshin Jiki?
Da alama mutane sun fara kauda kai daga kula da wasu turarukan kamshin jiki.Tsadar rayuwa ta sa mutane yanzu na cewa dole su nemi wasu dabarun, lura da yadda farashin irin wadannan kayayyaki na kula da tsaftar jiki ke kara tsada.Shirin Najeriya a Yau ya tattauna kan yadda mutane suka daina amfani da wasu kayan tsaftar jiki.
13:16 3/19/24
Dabarun Samun Sadarwa Da Intanet A Lokacin Da Aka Samu Tangarɗa
A makon da ya gabata da dama daga cikin yan kasa sun fuskanci  tangardar sadarwa musaman na intanet.A cewar wasu ‘yan Najeriya ya taba kasuwancinsu da dama da harkokin yau da kullum ga shi basu samu mafita ba, duk da hukumomi sun ce hakan ya faru ne sanadiyyar lalacewar wasu bututun karkashin ruwa ne.Shirin Najeriya a Yau ya lalubo muku hanyoyin da za ku samo mafita kafin a kammala irin wadannan gyare-gyare.
15:35 3/18/24
Matakan Kauce Wa Kamuwa Da Ciwon Ƙoda
Ƙoda na daga cikin sassan jikin dan adam da ke da mahimmanci wajen rayuwa mai lafiya da kwanciyar hankali.A haka kuma, wasu ke siyar da kodar tasu guda daya duk da yike masana kiwon lafiya na cewa ganganci ne yin hakan.A shirin Najeriya a Yau mun duba yadda za ku gane alamomin cutar koda da hanyoyin magance ta.
14:02 3/15/24
'Kalaman Buhari Na Yabon Gwamnatin Tinubu Ba Su Dace Ba'
Masu sharhi na ci gaba da tsokaci kan kalaman tsohon shugaba Buhari na jinjinawa gwamnatin Tinubu.Wasu na ganin akwai fannoni da dama da gwamnati ta samu tangarda, irinsu tsaro, tattalin arziki da sauransu.Shirin Najeriya a Yau ya yi fashin baki kan kalaman tsohon shugaban kasan.
14:59 3/14/24
Yadda Za Ku Yi Girke-giken Ramadan Da Kuɗi Kaɗan
Yanayin tsadar rayuwa da ake ciki ya sa dole a yi tattalin kudin da ake kashewa.An saba da Ramadana ana yawan yin girke-girke da kayan buda baki iri-iri, amma kuma wannan azumin ya zo cikin yanayi na tsadar kayan masarufi.Shirin Najeriya a Yau ya duba hanyoyin da za ku yi girke-girken da yawa yadda aka saba cikin sauki ba tare da kashe makudan kudade ba.
14:49 3/12/24
‘Yawan Karanta Littafai Na Sa Mutum Ya Fita Daban'
A wannan zamanin ba kowa ke da juriyar karanta littafai ba ko da kuwa ta waya ne, amma na alakanta hakan da shigowar fasahohin zamani da kimiyya.Masana na cewa yawaita karance-karance na taimakawa basirar dan adam musamman littafai na zahiri.Shirin Najeriya a Yau ya duba alfanun karanta littafai da wallafe-wallafe da ake yi wajen habaka kwazo da fikirar dan adam
11:19 3/11/24
Ranar Mata Ta Duniya: ‘Hakikanin Abin Da Mata Suke Bukata’
Irin wannan rana ta 8 ga watan Maris Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar mata ta duniya domin duba rawar da suke takawa a fannoni daban-daban.Wasu na ganin mata da dama da ke yiwa junan su hassada ya sa ba a samun ci gaban da ya kamata. yayinda ake ganin ya kamata a rika tallafawa ci gaban mata da kuma habaka tunaninsu.Majalisar Dinkin Duniya, ta ce  akwai mata kusan miliyan 342 da ke cikin barazanar fadawa  kangin talauci nan da shekarar 2030. Sai dai ta ya za a kaucewa hakan?Shirin Najeriya a Yau ya yi duba kan wannan rana da kuma yadda za a tallafi matan a fannoni daba-daban.
15:27 3/8/24
Yadda Rashin Wutar Lantarki Ke Kassara Sana'o'i
Sana’o’i na samun cikas da koma baya a wasu sassan Najeriya sakamakon rashin wutar lantarki. A yan kwanakin nan ana yawan kokawa da yadda wutar lantarki ke ƙara tabarbarewa.Masu sharhi na ganin da ace za a samu ingattaciyar wutar lantarki a Najeriya, to da cigaban da za a samu ya wice misali.Shirin Najeriya a Yau ya duba yadda rashin lantarki ke durkusar da kasuwanci a kasar.
14:00 3/7/24
Yadda Jama'a Ke Shan Wahalar Haɗa Lambar NIN da BVN a Bankuna
Tun bayan da CBN ta ba da umarnin a hada lambar NIN da BVN da asusun bankuna mutane ke ta turuwa domin ganin ba a kulle asusunsu ba.Masana na ganin wannan mataki zai yi tasiri sosai wajen matakan tsaro a Fannin hada-hadar kudade.Shirin Najeriya a Yau ya duba tasirin matakin da CBN ta yi umarni da yadda mutane ke shan wahalar gameda hakan.
12:04 3/5/24
Abin Da Ya Kamata Ku Sani Kafin Bayar Da Gudummawar Jini
Bayar da agajin jini, ko kyautar jini, daya ne daga cikin ayyukan da ake kwadaitar da yi.Ko mene ne dalilin da ya sa ake son mutane su rika bada agajin jini? Shirin Najeriya A Yau ya tattauna da masu abin cewa dangane da alfanun da ke tattare da bada agajin jini. 
14:39 3/4/24
Yadda Za Ku Mori Rayuwa Kafin Ku Wuce Shekara 30
A lokacin da matashi ke cikin kuruciya a tsakankanin shekara 30, ana sa ran ya cimma wasu burika a rayuwarsa.Toh amma a wannan yanayi da ake ciki, ta yaya matashi zai iya jin dadin rayuwarsa ta tafi kan tari kafin ya haura 30? Shirin Najeriya a Yau na tafe da shawarwarin mafita ga wadanda su ka wuce shekaru 30 amma babu kwakkarar madafa. 
14:50 3/1/24
Abin Da Zai Sa Farashi Ya Riƙa Sauka Bayan Ya Tashi
Yan kasa na kokawa kan yadda farashin komai ke hauhawa yayinda samun al’umma bai cika karuwa ba.Ya riga ya zama al’ada da zarar farashin wani abu a Najeriya ya hau sama, ba lallai ya sauko kasa ba.Shirin Najeriya a yau ya maida hankali kan sauyawar farashi abubuwa a Najeriya da yadda za a dauki matakin dakatar da hakan.
14:28 2/29/24